Kazar karfi: An saka makudan kudade ga duk wanda ya ayyana aiki daya da Buhari ya fara ya kammala

Kazar karfi: An saka makudan kudade ga duk wanda ya ayyana aiki daya da Buhari ya fara ya kammala

Kafar sadarwar zamani ta Tuwita ta shiga hargitsi tun jiya bayan da wata ma'abociya anfani da kafar mai suna Oke Omurhohwo (@stalyf) ta saka wata kazar karfi ta Naira dubu 20 ga duk wanda ya ayyana aiki daya tak da shugaba Buhari ya fara tun da farko ya kuma kammala tun hawan sa mulki.

Wannan kazar karfin dai da aka saka ta jefa masoya shugaba Muhammadu Buhari din cikin halin dimuwa inda har yanzu aka kasa samun mutun daya da ya samu nasarar lashe gasar.

Kazar karfi: An saka makudan kudade ga duk wanda ya ayyana aiki daya da Buhari ya fara ya kammala
Kazar karfi: An saka makudan kudade ga duk wanda ya ayyana aiki daya da Buhari ya fara ya kammala

KU KARANTA: Dan shekara 108 ya fadi sirrin tsawoncin rai

Legit.ng ta samu haka zalika cewa jim kadan bayan Oke Omurhohwo (@stalyf) ta saka gasar sai aka yi ta samun wasu mutanen suna kara nasu kudaden domin kyautar kudin ta kara yawa inda yanzu haka kudin sun kai kusan Naira dubu 400.

A wani labarin kuma, Kungiyar matasa ta wasanni a tarayyar Najeriya watau Youth Sports Federation of Nigeria (YSFON) reshen jihar Filato ta bayyana cewa ya zama wajibi fa ga shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya sake tsayawa takara a 2019.

Kungiyar da ta yi magana a ta bakin shugaban ta Idris Salihu Kwando ya bayyana cewa inda har ana so dukkan ayyukan alherin da shugaban kasar ya soma aiwatarwa su fara haifar da da mai ido to fa dole ne sai ya kara shafe shekaru hudu yana mulkin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel