Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da dogarin shugaba Buhari
Kamar yadda aka sani, dogarin shugaban kasa na daya daga cikin makusantan sa a kowace kasa domin kuwa kusan a iya cewa bacci sai kuma shiga ban daki ne kadai a wasu lokutan ke raba su.
A Najeriya, shugaba Muhammadu Buhari tun bayan lashe zaben sa ne dai ya nada Kanal Mohammed Lawal Abubakar a matsayin dogarin nasa.
KU KARANTA: Obasanjo ya kara caccakar Buhari
Legit.ng ta samu cewa a jiya ne ya yi bikin cika shekara 45 a duniya don haka ne ma muka tattaro maku wasu muhimman batutuwa akalla 5 game da shi da ya kamata ku sani:
1. Shi dai Kanal Mohammed Lawal Abubakar dan asalin garin Zaria ne ta jihar Kaduna.
2. Haka zalika Kanal Mohammed Lawal Abubakar yayi karatun digirin sa na farko ne a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria din inda ya karanta kwas din kimiyyar halittu watau Biological Science.
3. Kanal Mohammed Lawal Abubakar ya taba zama shugaban barikin sojoji na Giwa daga shekarar 2013 - 2014.
4. Haka ma Kanal Mohammed Lawal Abubakar ya halarci kwasa-kwasai da dama a ciki da wajen kasar nan ta Najeriya.
5. Daga karshe kuma Kanal Mohammed Lawal Abubakar yana da mata mai suna Fatima Musa da diya mace dai mai suna Aisha Nawal.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng