Kudin makaranta na ke nema inji wanda aka kama da buhu 80 na ganyen wiwi
- Hukumar NDLEA ta damke wani da buhuna rututu na tabar wiwi
- Wannan Bawan Allah yace yana harkar ne don ya biya kudin karatu
- Tun kwanaki matashin ya kammala karatun Digiri a wata Jamia'a
An yi ram da wani matashi a Jihar Edo da ake zargi da laifin saida tabar wiwi. Wannan Bawan Allah yace ya shiga harkar ne domin ya sama damar komawa makaranta yayi Digiri na biyu watau Digirgir.
Kamar yadda labari ya zo mana daga Jaridar Daily Trust, an kama Iredia Austin da buhuna 82 na ganyen wiwi. Austin yace tun 2011 yake wannan harkar saboda ya iya biyawa kan sa kudin makaranta saboda rashin hali.
KU KARANTA: Sanatan da ake nema ya halarci zaman Majalisa
Iredia Austin yayi karatu ne a Jami'ar Ambrose Ali da ke Ekpoma kuma bayan ya kammala yayi hidimar kasa. A lokacin da ya gama Jami'a, yace ya daina harkar wiwi amma yanzu dole ta sa ya koma saboda ya koma karatu.
Hukumar NDLEA ta dai yi ram da wannan Bawan Allah dauke da ganyen wiwi na kilo 762 a cikin Jihar Edo. Yanzu za a maka saurayin nan a Kotu domin ya amsa laifin sa kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng