Za'a fara tiyatar dashin koda a wannan asibitin koyarwar ta Najeriya
Mahukunta a babbar asibitin koyarwa ta jami'ar Najeriya dake a garin Enugu, babban birnin jihar Enugu dake a yankin kudu maso gabashin Najeriya sun bayyana cewa asibitin za ta fara yin tiyatar dashin koda ga marasa lafiya masu bukata.
Wannan dai, kamar yadda muka samu yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da asibitin ta fitar dauke da sa hannun kwararrun likitoci shidda a cikin satin da ya gabata.
KU KARANTA: Najeriya za ta fi dadi in ba 'yan PDP - Lai Mohammaed
Legit.ng ta samu kuma cewa hukumar asibitin ta zabtare kudin yin tiyatar daga kusan Naira miliyan 11 ya zuwa Naira miliyan 3 da rabi wanda a cewar su sun yi hakan ne domin samar da sauki ga masu bukarar hakan.
Haka ma dai hukumar gudanarwar asibitin ta zayyana cewa za su soma yin tiyatar ne a ranar 7 zuwa 14 ga watan Yulin da ke tafe don haka dukkan mai bukata sai ya garzaya asibitin domin karin bayani.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng