An kori dan sandan da ya bindige wani yaron mota daga aiki
- Hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Imo, ta kori wani jami'inta, Saja Abu Itam, saboda kisan wani yaron mota
- Fusatattun matasa sun kone ofishin hukumar 'yan sanda na Okwelle, inda abin ya faru, bayan harbe yaron motar
- Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Chris Ezike, ya ce, Saja Itam, da ragowar 'yan sanda da suka yi aiki a wurin da abin ya faru, dole su fuskanci hukunci
Hukumar 'yan sanda reshen jihar Imo ta kori wani mai mukamin saja, Abu Itam, daga aiki bayan ya saka bindigar sa kirar AK-47 ya bindige wani yaron mota, Ifeanyi Okafor, ranar 9 ga watan Fabrairu, 2018.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:00 na safe a wata kwana dake daf da ofishin hukumar 'yan sanda na Okwelle dake karamar hukumar Onuimo ta jihar Imo.
Jaridar Punch ya rawaito cewar, cacar baki ce ya shiga tsakanin jami'in dan sandan da yaron motar, bayan an tsayar da motar su ta dakon kaya.
Saja Itam da abokan aikinsa mutum sun tsayar da motar su marigayin mai lamba AAH 229 XA tare da ragowar motoci, amma sai suka bukaci motar su Okafor ta tsaya bayan sun sallami ragowar motocin.
A yayin cacar bakin neman sanin dalilin tsayar da su ne sai Itam ya fitar da bindigar sa ya harbi Okafor sau uku sannna ya tsere.
DUBA WANNAN: Muna son sanin adadin kudin da EFCC ta kwato da kuma inda suke ajiye - Ministar kudi
Kisan Okafor ya harzuka matasan yankin har ta kai sun kone ofishin hukumar 'yan sanda na Okwelle. Saidai anyi nasarar shawo kan wutar kafin tayi ta'adi mai yawa.
A yau, Litinin, kwamishinan 'yan sanda a jihar, Chris Ezike, ya tabbatar da cewar sun kori Itam daga aiki tare da bayar da tabbacin cewar za a gurfanar da shi da ragowar abokan aikinsa a ranar gaban shari'a.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng