Faifan Bidiyo: Yadda Dangote ya sha rawa a wajen walimar bikin diyar sa Fatima

Faifan Bidiyo: Yadda Dangote ya sha rawa a wajen walimar bikin diyar sa Fatima

Faifan bidiyo ya fita inda yake dauke da shahararren hamshakin mai kudin nan na farko a nahiyar Afrika Alhaji Aliko Dangote yana ta tikar rawa a wajen walimar bikin diyar sa Fatima Dangote da ta gudana a jiya, garin Legas.

Mun samu dai cewa shahararren mai kudin dai ya taka rawar ne yayin da fitaccen mawakin nan dan asalin Najeriya Mai suna Davido ke cashewa da wakar sa mai suna 'Fia'.

Faifan Bidiyo: Yadda Dangote ta sha rawa a wajen walimar bikin diyar sa Fatima
Faifan Bidiyo: Yadda Dangote ta sha rawa a wajen walimar bikin diyar sa Fatima

KU KARANTA: An ci an sha: Manyan mutane sun halarci bikin diyar Dangote

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a ranar Juma'ar da ta gabata ne dai aka gudanar da walimar kayataccen bikin nan na fada aji na diyar hamshakin mai kudin nan na nahiyar Afrika watau Fatima Dangote da kuma angon ta Jamilu Abubakar a birnin Ikko na jihar Legas.

Walimar dai ta tara dukkan manyan kasar nan har ma da na kasashen waje kama da ga 'yan kasuwa, yan siyasa zuwa ga manyan jami'an gwamnati akowane mataki na kasar.

Wasu daga cikin wadanda suka halarci bikin dai sun hada da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, tare da matar sa Dolapo Osibajo, sai kuma hamshakin mai kudin nan Bill Gates da kuma matar sa Melinda Gates.

Sauran sun hada da uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari, Sarkin Kano Sanusi Lamido, gwamnoni da Sanatoci da 'yan majalisar wakillai da dai sauran su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng