An ci-an sha: Hotunan manyan mutanen da suka halarci walimar auren diyar Dangote da angon ta
- Hotunan manyan mutanen da suka halarci walimar auren diyar Dangote da angon ta
- A jiya Juma'a ne dai aka gudanar da walimar kayataccen bikin nan na fada aji a birnin Ikko
- Walimar dai ta tara dukkan manyan kasar nan har ma da na kasashen waje
A jiya Juma'a ne dai aka gudanar da walimar kayataccen bikin nan na fada aji na diyar hamshakin mai kudin nan na nahiyar Afrika watau Fatima Dangote da kuma angon ta Jamilu Abubakar a birnin Ikko na jihar Legas.
KU KARANTA: Aina'u Ade ta bayyana lokacin auren ta
Walimar dai ta tara dukkan manyan kasar nan har ma da na kasashen waje kama da ga 'yan kasuwa, yan siyasa zuwa ga manyan jami'an gwamnati akowane mataki na kasar.
Wasu daga cikin wadanda suka halarci bikin dai sun hada da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, tare da matar sa Dolapo Osibajo, sai kuma hamshakin mai kudin nan Bill Gates da kuma matar sa Melinda Gates.
Sauran sun hada da uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari, Sarkin Kano Sanusi Lamido, gwamnoni da Sanatoci da 'yan majalisar wakillai da dai sauran su.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng