Kotu zata yankewa duk wanda ya kashe musulmi hukuncin daurin rai da rai

Kotu zata yankewa duk wanda ya kashe musulmi hukuncin daurin rai da rai

- Wata babbar kotun kasar India dake jihar Jharkhand ta yankewa wasu mutane 11 hukuncin daurin rai da rai, saboda kama su da aka yi da kisan wani musulmi saboda yana tallar naman shanu a shekarar da ta gabata

Buhari ya ce zaibi duk wata hanya domin ceto Leah Sharibu
Buhari ya ce zaibi duk wata hanya domin ceto Leah Sharibu

Wata babbar kotun kasar India dake jihar Jharkhand ta yankewa wasu mutane 11 hukuncin daurin rai da rai, saboda kama su da aka yi da kisan wani musulmi saboda yana tallar naman shanu a shekarar da ta gabata.

DUBA WANNAN: Kotun kasar Holland ta ce baza ta hukunta wadanda suka furta kalaman kyama ga musulunci ba

Mutanen sun lakadawa Alimuddin Ansari, mai shekaru 55, dukan tsiya, inda har sai da ya rasa ransa, saboda kawai sun same shi yana sayar da naman shanu.

Wannan shine karon farko da gwamnatin India ta yanke hukunci akan mutanen da suke sanya ido akan masu cin naman shanu, duk kuwa da cewa an shafe shekaru da yawa ana samun kai hare hare akan musulmai masu sayar da naman.

Wanda suke bin addinin Hindu sun dauki Saniya a matsayin wata halitta mai tsarki wanda har ya kai ga mawar da wasu suna bauta mata, sannan kuma suka haramta kisan ta a da dama daga cikin jihohin kasar ta India, ciki kuwa har da jihar Jharkhand.

Sau da yawa masu bautar saniyar suna kai hare hare akan masu cin naman shanu da kuma masu sayar dashi a kasar ta India, sannan kuma hukuma bata fiya daukan mataki akan wanda ta kama da laifin kai harin ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng