Majalisar Dinkin Duniya tayi murna da sakin 'yan matan Dapchi, tayi kira da gwamnati ta hukunta wadanda ke da hannu cikin satar matan

Majalisar Dinkin Duniya tayi murna da sakin 'yan matan Dapchi, tayi kira da gwamnati ta hukunta wadanda ke da hannu cikin satar matan

- Majalisar Dinkin Duniya ta yaba da kokarin gwamnati wajen ceto yan matan Dapchi guda 104

- Sakataren Majalisar, Antonio Guteres ya kuma shawarci gwamnatin tarayyah ta tabbatar da cewa an sako sauran yan matan

- Gutures kuma ya kara da cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta dauki mataki a kan wadanda ke da hannu cikin satar yan matan

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteres ya yi yabawa kokarin gwamnatin tarayya wajen ceto yan matan makarantar sakandire na Dapchi da yan Boko Haram suka sace a cikin kwanakin nan.

Majalisar Dinkin Duniya ta yabawa gwamnati bisa ceto 'yan matan Dapchi
Majalisar Dinkin Duniya ta yabawa gwamnati bisa ceto 'yan matan Dapchi

A wata sanarwa da Sakataren ya bayar a birnin New York da ke Amurka, ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta gudanar da bincike kana ta hukunta duk wadanda aka samu da hannu cikin satar yaran kamar yadda NAN ta ruwaito.

KU KARANTA: Soji sun arce a guje bayan sun hango ‘yan Boko Haram, inji Mutanen Dapchi

Sakataren kuma ya kara jadada cewa ya kamata gwamnatin Najeriya tayi duk mai yiwuwa don ganin cewa an dawo da sauran yaran da ke tsare a tare da yan kungiyar na Boko Haram don mayar da su ga iyalan su.

Ya kuma yi kira ga "mahukunta a Najeriya suyi gagawa wajen hukunta wadanda ke da hannu cikin wannan rashin adalcin".

A wata rahoton, Legit.ng ta ruwaito cewa Hukumar sojin Najeriya a ranar Laraba, 21 ga watan Maris ta mika yan mata 106 zuwa ga gwamnatin tarayya.

Guda 104 cikin wadanda aka sako yan makarantar sakandire na Dapchi ne, sai kuma yaro na miji daya da mace daya da yan Boko Haram din suka sako.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164