Saudiyya ita ce kasar da tafi ko ina hada fitina a duniya - inji Al Khamaini

Saudiyya ita ce kasar da tafi ko ina hada fitina a duniya - inji Al Khamaini

- Ayatullah Al Khamaini ya bayyana kasar Saudiyya a matsayin kasar da ta fi ko ina hada fitina a duniya

- Ya kuma karyata kasar Amurka da ikirarin da take na cewar ita tayi maganin 'yan ta'addar DAESH

- Ya ce tilas ne duniya ta jinjina wa kasar Iran akan kokarin da tayi na kawar da zaluncin 'yan ta'addar na DAESH wanda suka addabi yankin gabas ta tsakiya

Saudiyya ita ce kasar da tafi ko ina hada fitina a duniya - inji Al Khamaini
Saudiyya ita ce kasar da tafi ko ina hada fitina a duniya - inji Al Khamaini

Shugaban addinin musulunci na kasar Iran, Ayatullah Al-Khamaini ya tabbatar da cewa, tilas ne duniya ta jinjina musu, domin kuwa kasar ta taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya a duniyar musulunci. Ta hanyar yin maganin 'yan ta'addar DAESH da suke yankin gabas ta tsakiya.

DUBA WANNAN: Janna yarinyar da ta ke neman zama barazana ga kasar Isra'ila

Kasar Iran inda mabiya addinin shi'a suka fi yawa, kasar tana yin fito na fito da kasar Saudiyya, inda ta ke babbar cibiyar mabiya sunni ta duniya, dalilin da yasa suke ta faman goyawa bangarori mabambanta baya a rikicin kasashen Iraki, Labanon, Sham da kuma kasar Yamen.

Kasar Iran tana zargin kasar Saudiyya da bawa 'yan ta'addar tallafi, wadanda ke cigaba da zubar da jinin dubban al'umma a yankin gabas ta tsakiya, sai dai kuma kasar Saudiyyar ta yi watsi da tuhumar da kasar Iran din take yi mata.

Da yake bayani a babbar tashar gidan talabijin na kasar Iran, Al-Khamaini ya ce:

"Tilas ne a yabawa kasar Iran, don ta bada gagarumar gudunmawa wajen kawo zaman lafiya a duniyar Islama, ta hanyar yin maganin 'yan ta'addar da suka addabi yankin gabas ta tsakiya. Kasar Amurka tana ta karereyin cewar ita ce ta yi maganin DAESH a yankin, hakan ba gaskiya bane, saboda kasar mu ce ta kori 'yan ta'addar, wanda suke sune 'yan gaban goshin kasar Saudiyya, wacce a yanzu haka babu kasa fitinanniya kamar ta".

Bayanin na Al-Khamaini yazo a dai dai lokacin da, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya karbi bakuncin yariman kasar Saudiyya mai jiran gado, Muhammad bin Salman, domin neman hanyar da za a hana kasar Iran shiga harkokin gabas ta tsakiya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng