Janna yarinyar da ta ke neman zama barazana ga kasar Isra'ila

Janna yarinyar da ta ke neman zama barazana ga kasar Isra'ila

- Janna yarinya 'yar shekara 11 da haihuwa ta nuna jarumta wurin zabge wani sojan Isra'ila da mari

- Kasar Isra'ila ta tsorata da lamarin yarinyar, inda kasar ta bayyana yarinyar a matsayin barazana a gareta

Janna yarinyar da ta ke neman zama barazana ga kasar Isra'ila
Janna yarinyar da ta ke neman zama barazana ga kasar Isra'ila

Wata yarinya 'yar shekaru 11 da haihuwa 'yar asalin kasar Falasdin ta shararawa wani sojan Isra'ila mari, inda hakan yayi mutukar girgiza kasar Isra'ila, inda a yanzu haka kasar ta bayyana yarinyar a matsayin barazana babba a gareta.

DUBA WANNAN: Sama da mutum 100,000 suka yi kaura daga jam'iyyar PDP da APC zuwa jam'iyyar SDP

A rahoton da wata tashar yada labarai ta Isra'ila ta fitar, ta bayyana cewa an kulle yarinyar mai suna Janna, wacce ake ganin ta lashe lambar yabo ta zama maras tsoro.

Hukumar harkokin wajen kasar Isra'ila ta bayyana Janna, wacce ta fito daga kauyen Nabi Salih a yankin yammacin gabar kogin Jordan, a matsayin baraza mai karfi ga kasar Isra'ila.

A kwanakin baya yarinyar ta dauki hotuna da bidiyo na yadda sojojin kasar Isra'ila suke cin zarafi tare da azabtar da Falasdinawa, inda ta yada a kafafen sadarwa da shafukan Intanet.

Miliyoyin mutane na sassa daban-daban na duniya sun kalli wadannan hotunan da bidiyo wanda Janna ta saka, inda mutane suka dinga Allah wadai da irin abinda kasar ta Isra'ila ta ke yi.

Hakan da yarinyar ta yi yayi matukar razana kasar Isra'ila inda ta bayyana yarinyar a matsayin "Babbar Barazana gareta".

A wata hira da aka yi da ita da kafar sadarwa ta Anadolu Agency, Janna ta ce babban burinta shine ta zama "Muryar Yaran Falasdinu".

A rahoton da kafar sadarwa ta Isra'ila ta fitar, ta ce kotu ta yanke wa Janna wacce a yanzu haka al'ummar duniya ke mata kallon "Jarumar Falasdinu", hukuncin wata 8 a kurkuku.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng