Yakubu Dogara ya bayyana matsayar sa akan sake fasalin kasar nan

Yakubu Dogara ya bayyana matsayar sa akan sake fasalin kasar nan

Kakakin majalisar wakillai Mista Yakubu Dogara tare da hadin gwuiwar wani fitaccen shugaban kabilar yarbawa a karkashin inuwar kungiyar Yoruba Unity Forum mai suna Cif Dipo Jemileyin ya bayyana cewa shima yana goyon bayan a sake fasalin kasar nan a bangarori da dama.

Mista Yakubu Dogara tare Cif Dipo sun yi wannan kalaman ne a lokuta daban daban dukkan su yayin da suke gabatar da jawaban su a wajen wani taro da ake yi domin nemo hanyar tabbatar da cigaban kasar karo na uku a garin Abuja da wata kungiyar mai rajin kare dimokradiyya a Nahiyar Afrika ta shirya.

Yakubu Dogara ya bayyana matsayar sa akan sake fasalin kasar nan
Yakubu Dogara ya bayyana matsayar sa akan sake fasalin kasar nan

KU KARANTA: Yadda dan sanda ya kashe soja a Najeriya

A wani labarin kuma, Babbar kungiyar nan ta addinin Islama a Najeriya ta Jama’atu Nasril Islam, karkashin jagorancin Sarkin musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III ya bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya farfado daga doguwar sumar da yayi domin ya cigaba da mulkin kasar nan yadda ya kamata musamman ma wajen fannin tsaro.

Wannan kiran dai kamar yadda kugiyar ta ayyana ya zama dole ne biyo bayan abun da ta kira kisan kiyashin da ake cigaba da yiwa musulmi a sassan kasar nan ciki hadda karamar hukumar Bassa ta jihar Filato.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng