Tirka-tirka: Jam'iyyar APC ta dauko hanyar watsewa a jihar Imo
Dandalin siyasa ya fara zafafa a jihar Imo dake yankin kudu maso gabashin kasar nan biyo bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a karshen satin da ya gabata a garin Owerri, babban birnin jihar ta Imo inda wasu jiga-jigan jam'iyyar suka fice daga taron ana tsakar yin sa.
Mun samu dai cewa wadanda suka fice daga taron sun hada da babban jami'in Sakataren gudanarwa na jam'iyyar a mataki na kasa baki daya mai suna Osita Izunaso da kuma zababbun Sanatocin jam'iyyar Ifeanyi Araraume da Benjamin Uwajiumogu.
KU KARANTA: Abdussalami ya yabawa salon mulki El-Rufa'i
Legit.ng ta samu hakan dai kamar yadda majiyoyin mu suka labarta mana na da alaka da rashin adalcin da suke ganin an yi masu ko kuma na cikin yi masu a jihar.
A wani labarin kuma, Tsohon gwamnan jihar Adamawa kuma jigo a jam'iyya mai mulki ta APC, Murtala Nyako ya gargadi shugabannin jam'iiyar ta APC da su guji maimaita abun da ya jao rugujewar jam'iyyar PDP a gabanin zaben 2015 ta hanyar tabbatar da yin adalci ga kowa.
Gwamnan kamar yadda muka samu ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ziyarar ta'aziyyar da ya kai wa iyalan tsohon gwamnan jihar Saleh Michika a a ranar asabar din da ta gabata.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng