Danqari! Wani limami yaje lahira ya dauko hoton aljanna ya dawo yana sayarwa 5,000 a kallo-kallo

Danqari! Wani limami yaje lahira ya dauko hoton aljanna ya dawo yana sayarwa 5,000 a kallo-kallo

- Ana raina wa mabiya addinai wayau a lokuta da dama

- Pastor sun maida kirista sljihun tatsa

- Yace wai yaje Aljanna ya dauko hotuna

Danqari! Wani limami yaje lahira ya dauko hoton aljanna ya dawo yana sayarwa 5,000 a kallo-kallo
Danqari! Wani limami yaje lahira ya dauko hoton aljanna ya dawo yana sayarwa 5,000 a kallo-kallo

Annabi Mboro na cocin Incredible Miracles and Ministiries dake Johannesburg a kasar Afirka ta kudu ya zo da sabuwar mu'ujiza daga sama, inda yace yaje lahira ya amso wahayi, kuma an nuna masa aljanna harma ya dauko hotuna.

Sai dai matsalar shine, sayar da hotunan yake yi maimakon ya nuna wa mabiya kyauta. Rand 5,000 yake sayar dasu domin masu bukatar gani ko sha'awar suje aljannar.

DUBA WANNAN: Ya auri maciji amma daga baya ya kashe shi

Hadimin mai-tsarki Mboro dai, Mista Nkuna, yace a ranar Easter ta bana ne wannan hamshakin Pasror ya sami zuwa sama inda Allah yayi masa ilhama har yayi gane-gane ya dauko hotuna da wayar salularsa, ta Samsung Galaxy, ya kuma hawo hadari da gajimare ya dawo a dare daya.

A dai wannan zamani, da wuya mutane su yadda da irin wannan shaci fadi, sai dai ga mabiya irin wadannan annabawa, abin haka yake ba tantama, saboda ba ilimi ko tunani suke aiki dashi ba, makahon imani ne da tsoron mutuwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng