Gulma: Mace daga Angola ta buge wata macen daga Najeriya a mata da suka fi kowa kudi a Afirka

Gulma: Mace daga Angola ta buge wata macen daga Najeriya a mata da suka fi kowa kudi a Afirka

- Isabel dos Santos, diyar tsohon shugaban kasar Angola, Jose Eduardo dos Santos, ta zama mace wadda tafi kowa kudi a Afirika

- A cikin masu kudi 23 na Afirika, wadanda masu hasashe suka kididdiga a 2018, biyu ne kadai mata, Isabel dos Santos, da Folorunsho Alakija

- Isabel dos Santos, tanada a kimanin $2.7, inda tayo kasa daga abunda take dashi a bara, kimanin $3.2

Gulma: Mace daga Angola ta buge wata macen daga Najeriya a mata da suka fi kowa kudi a Afirka
Gulma: Mace daga Angola ta buge wata macen daga Najeriya a mata da suka fi kowa kudi a Afirka

Isabel dos Santos, diyar tsohon shugaban kasar Angola, Jose Eduardo dos Santos, ta zama mace wadda tafi kowa kudi a Afirika, a kiyashi na masu hasashe, a shekarar 2018.

A cikin masu kudi 23 na Afirika, wadanda masu hasashe suka kiyasta, a 2018, biyu ne kadai mata, Isabel dos Santos, da Folorunsho Alakija, wanda bai canza ba daga bara. Isabel dos Santos, tanada a kimanin $2.7, inda tayo kasa daga abunda take dashi a bara, kimanin $3.2.

Rahotanni sun nuna tayo kasane sakamakon Bankin BIC, na Angola, da yayi kasa; Darajarsa ta tayi kasa a shekarar 2016, a lokaci mai tsanani da kasar mai arzikin Mai ke fuskanta. Isabel ta doke Folorunsho Alakija, wadda keda kimanin $1.6bn, ya dogara ne Kamfanin Famfa Oil.

DUBA WANNAN: Boko Haram ta aiko sako ta wayoyin wadanda suka sace

Majiyar Legit.ng ta bayyana cewa, shugaba kuma Jagoran Kamfanin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote, shine aka bayyana a matsayin wanda yafi kowa arziki a Afirika a shekara ta bakwai, Jaridar masu hasashe.

Dangote wanda keda Kamfanin Siminti a Najeriya da kayayyaki mai cin gashin kansa, wada keda kimanin $12.2bn, a kiyasin masu hasashe, yayi sama da $100m fiye da abunda yake dashi a shekarar data wuce.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng