'Yan sandan Najeriya sun yi galaba kan wani hatsabibin tsageran Neja Delta

'Yan sandan Najeriya sun yi galaba kan wani hatsabibin tsageran Neja Delta

Jami'an 'yan sandan Najeriya dake a bangaren tattara bayanan sirri na shiyyar jihar Ribas sun sanar da samun nasarar kashe kasurgumin hatsabibin tsageren Neja Delta bayan ba-ta-kashi na tsawon lokaci da suka yi dashi.

Tsageran mai suna Prosper David 'yan sandan sun ce sai da suka ji ma sa ciwo a lokacin da yake kokarin tserewa kafin daga bisani ya mutu sakamakon ciwon da aka ji masa.

'Yan sandan Najeriya sun yi galaba kan wani hatsabibin tsageran Neja Delta
'Yan sandan Najeriya sun yi galaba kan wani hatsabibin tsageran Neja Delta

KU KARANTA: Ku sadu da 'Jamboy' - angon Fatima Dangote

Legit.ng ta samu cewa 'yan sandan na Najeriya sun zayyana wasu hare-hare da kuma satar manyan mutane da suka hada da wata matar Mista Tina Bob Manuel a cikin watan Nuwamban bara a matsayin ayyukan ta'addancin da ya aikata.

A wani labarin kuma, Wani alkalin babbar kotun tarayya dake zaman ta a garin Legas a unguwar Igbosere mai suna mai shari'a Oluwatoyin Ipaye a yau din nan ya yanke wa wani dillalin gidaje mai suna Babatunde Habeeb hukuncin daurin shekaru 1,230 a gidan yari.

Alkalin da ya ke yanke hukunci akan mai laifin ya gano cewa Mista Babatunde Habeeb ya damfari wasu mutane ne su 101 kudaden da suka kai darajar Naira miliyan 28 da sunan zai samar masu gidan zama.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng