Kungiyar Izala ta fara gudanar da gasar kacici-kacici karo na farko a jihar Kaduna
A ranar Litinin 12 ga watan Maris, 2018, Kungiyar jama'atu Izalatil-bid'ati Wa ikamatis-Sunnah ta kasa karkashin jagorancin Shugaba As-Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau ta bude gasar kacici-kacicin addini a Dr Ahmad Muhammad Makarfi Qur'anic complex dake Kinkinau a jihar Kaduna.
Ita dai wannan gasar ita ce irinta ta farko a tarihin Kungiyar tun bayan kafuwar ta, kimanin shekaru arba'in.
Taron ya samu halartar manyan malamai daga sassan kasar nan.
Ana gudanar da wannan taron ne karkashin kulawar Daraktan sashen ilimi da ilmantarwa na Kungiyar Dr Abdullahi Saleh Pakistan Kano.
Tuni dai bayan bude taron aka ci gaba da gudanar da gasar a bangarori biyu Na maza da mata.
DUBA WANNAN: An kama bindigu a motar kamfen din wani dan takarar majalisar a jam'iyyar APC
Ana sa ran gasar zata kwashe tsahon kwanaki biyar cif ana gabatarwa, daga nan sai ayi taron rufewa da raba gwababan kyaututtuka ga wadanda suka samu nasara a ranar Asabar mai zuwa wato 17/03/2018.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng