Naira 12 biliyan: Yadda ta kaya tsakanin Ali Modu Sheriff da hukumar EFCC
Biyo bayan gayyatar da hukumar nan dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC tayi wa tsohon Gwamnan jihar Borno Ali Modu Sheriff a ranar Litinin game da neman ba'asin yadda aka yi ya sayi jirgin Naira biliyan 12, bayanan yadda ta kaya sun fara bayyana.
Wata majiya mai tushe daga ofishin EFCC ta shaida mana cewa da Sanata Sheriff din ya je hedikwatar hukumar ya mika wasu takaddun sa ne ga hukumar a wani yunkurin sa na ganin cewa ya wanke kansa daga dukkan zargi.
KU KARANTA: An kama budurwa da wayar satar ansa cikin dan tofi
Legit.ng ta samu cewa kuma biyo bayan hakan ne sai hukumar ta EFCC ta bayar da shi beli bayan tayi duba da irin matsayin sa a al'umma yayin da take kuma cigaba da bincike kan lamarin.
A wani labarin kuma, Wani matashi wanda yake da ra'ayin fitowa takarar shugaban kasa a zaben 2019 mai suna Adamu Garba II ya fito ya bayyana cewa yanzu dai kam ta tabbata cewa ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ba ke mulkar Najeriya.
Matashin dai ya bayyana hakan ne a yayin da yake maida martani a shafin sa na Tuwita mai adreshin @adamugarba game da kalaman shugaban da ya yi a jihar Benue inda yace yayi mamaki da aka gaya masa cewa shugaban 'yan sandan Najeriya yayi fatali da umurnin da ya bashi na komawa jihar Benue din.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng