Jarabawar Jamb: Hukumar tsaron farar hula ta kama wata mace da waya cikin dan tofin ta

Jarabawar Jamb: Hukumar tsaron farar hula ta kama wata mace da waya cikin dan tofin ta

Jami'an tsaron farar hula na gwamnatin tarayya Nigerian Security and Civil Defence Corps, NSCDC shiyyar garin Abuja, babban birnin tarayya a jiya sun gabatar da wasu mutane biyu ga manema labarai bisa laifin aikata satar ansa yayin gudanar da jarabawar share fagen shiga jami'a watau Unified Tertiary Matriculation Examination (UTME).

Kamar yadda muka samu kuma, cikin wadanda aka gurfanar din sun hada da wata mace wadda aka zarga da boye wayar salula a cikin dan tofin ta wadda kuma take anfani da ita wajen satar ansa a yayin jarabawar.

Jarabawar Jamb: Hukumar tsaron farar hula ta kama wata mace da waya cikin dan tofin ta
Jarabawar Jamb: Hukumar tsaron farar hula ta kama wata mace da waya cikin dan tofin ta

KU KARANTA: Za'a maka gwamnatin Buhari kotu

Legit.ng ta samu haka zalika cewa macen da aka zarga ta ansa laifin ta amma kuma sai ta nemi ayi mata rangwame musamman ma ganin cewa ba halin ta bane.

A wani labarin kuma, Hukumar nan dake da alhakin shirya jarabawar kammala makarantar Sakandare ta yammacin Afrika watau West African Examination Council, WAEC a jiya ta sanar da fara fitar da sakamakon jarabawar da ta gudanar ga dalibai a cikin farkon shekarar nan ta 2018.

Da yake sanar da hakan a babbar hedikwatar hukumar dake garin Legas, shugaban hukumar Mr. Isaac Adenipekun ya bayyana cewa cikin dalibai 11,307 da suka zauna jarabawar, akalla mutane 1,937 ne kacal suka samu nasarar lashe darussa 5 zuwa sama da suka hada da Turanci da kuma Lissafi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel