Mahaifiyar Maryam Sanda, Maimuna Aliyu ta sake shiga cikin wata tsomomuwa

Mahaifiyar Maryam Sanda, Maimuna Aliyu ta sake shiga cikin wata tsomomuwa

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zaman ta a unguwar Jabi, a jiya ta nuna rashin jin dadin ta zuwa ga lauyan dake kare mahaifiyar matar nan da ake zargi da kashe mijin ta Bilyaminu watau Maryam Sanda mai suna Maimuna Aliyu bisa raina mata wayau.

Mun samu dai cewa ita dai Maryam Aliyu hukumar nan dake yaki da masu laifukan cin hanci da rashawa ne mai zaman kanta wata ICPC ta shigar da ita kara bisa laifuka 3 ciki hadda zamba cikin aminci da damfara da kuma sayar da kadarorin da ba na ta ba.

Mahaifiyar Maryam Sanda, Maimuna Aliyu ta sake shiga cikin wata tsomomuwa
Mahaifiyar Maryam Sanda, Maimuna Aliyu ta sake shiga cikin wata tsomomuwa

KU KARANTA: Yan majalisar APC suna munafuntar Buhari - Sanata Adamu

Legit.ng ta samu cewa sai dai alkalin kotun ya nuna matukar bacin ran sa bayan da lauyan da ke kare ta mai suna Osuobeni Akponimisingha ya shaida masa cewa bai samu damar kawo dukkan shaidun sa 11 ba kamar yadda yayi alkawin inda kuma alkalin ya umuci a ci shi tara.

A wani labarin kuma, Gamayyar kungiyoyin matasan arewacin Najeriya a jiya sun yi wani taro inda suka kaddamar da wani gangami domin yaki da abun da suka kira yadda wadanda ba 'yan jiha ba da kabilu suke mamaye dukkan guraben ayyukan yan asalin jihar.

Kamar dai yadda muka samu, kungiyoyin matasan sun zargi cewa kawo yanzu kusan kaso 70 cikin dari na ayyukan jihar Kano kabilu ne da kuma 'yan wasu jihohi ne suke rike da su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng