Duk wanda aka kama ya mallaki budurwar danko zai ta fi kurkuku - Zambia
- Gwamnatin kasar Zambia ta yiwa al'ummar kasar kashedi akan mallakar 'yar tsana
- Gwamnatin Zambia ta yi barazanar daure duk wanda aka kama da 'yar tsana a gidan kaso
Gwamnatin kasar Zambia ta ce za ta daure duk dan kasar da aka kama shi ya mallaki ‘yar tsanar da aka kirkira saboda namiji ya rika jima’ai da ita a gidan kaso.
Wannan yana cikin mataki na farko da gwamnatin kasar ta dauka dan hana yaduwar ‘yar tsanar a cikin kasar.
“Kada kowa ya sayar da ita a kasuwa kuma kada kowa ya saye ta, saboda duk wanda aka kama ya mallake ta za 'dan'dani kuden sa,' inji gwamanatin kasar.
A watan da ta gabata ne gwamnatin kasar Zambia ta fara farautar masu sayar da ‘yar tsanar a cikin kasar.
KU KARANTA : Rikicin Makiyaya: Ba dai-dai bane a rika daukan Fulani a matsayin 'yan ta'adda - Atiku
"A matsayin kasar Zambia na Kristoci, barin ‘yar tsana ta yadu a cikin al'ummar kasar babban laifi ne a gaban Ubangiji," inji Ministan harkan Addini na kasar, Mista Godfridah Sumaili .
Saya da sayar da ‘yar tsana ya saba dokar kasar a Zambia.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng