Yan sanda sun kashe barayi 2, sun kuma kama wasu 6 a cikin garin Abuja
Jami'an rundunar yan sandan Najeriya shiyyar babban birnin tarayyar Najeriya sun sanar da samun nasarar kashe wasu gawurtattun barayi biyu sannan kuma suka kama wasu akalla shidda a yayin artabun da suka yi da su a unguwar Lugbe, garin Abuja.
Da yake karin haske game da batun, Kwamishinan yan sandan birnin tarayyar, Sadiq Bello ya bayyana cewa a ranar Asabar 10 ga watan Maris jami'an yan sandan sa sun yi bata kashi da wasu gungun barayain da suka kai kusan 30 biyo bayan korafin da suka samu daga mutanen unguwar ta Lugbe.
KU KARANTA: Manyan lauyoyi sun yi fata-fata da majalisar dattijai
Legit.ng haka zalika ta samu cewa wadanda aka kama sun hada da Jim Williams, Emmanuel Okoro, Emeka Nwafor, Okey David, Onwunali ThankGod, da kuma Uchena Chukwuma kuma an kama su da bindigun gargajiya da kuma harsasai.
A wani labarin kuma, shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a jiya Talata ya bayyana cewa kungiyar ta'addancin Boko Haram kawo yanzu ba ta da wani katabus din da za'a rika maganar ta a kasar duk kuwa da sabbin hare-haren da ta kai a makarantar kwana ta 'yan mata a Dapchi da kuma kauyen Rann a jihar Borno a yan kwanakin nan.
Sai dai da ya ke karin haske, shugaban kasar ya bayyana cewa irin wadannan hare-haren na ta'addancin babu gwamnatin da ke iya hana yin su dun kuwa da irin tsaron da ke gare ta a kasa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng