Naira 13.5 miliyan: Manyan yan gwagwarmaya, gawurtattun lauyoyi sun yi kaca-kaca da majalisar dattijai

Naira 13.5 miliyan: Manyan yan gwagwarmaya, gawurtattun lauyoyi sun yi kaca-kaca da majalisar dattijai

Wasu daga ckin manyan yan gwagwarmaya da kuma gawurtattun lauyoyin kasar Najeriya sun yi kaca-kaca da majalisar dattijai bisa ga makudan kudaden alawus din da suke ansa duk wata da suka kai Naira miliyan 13.5 kamar dai yadda daya daga Sanatocin Sanata Shehu Sani ya fada.

Mun samu dai cewa manyan Lauyoyi kamar Mista Femi Falana, Mista Yusuf Ali da kuma Farfesa Itse Sagay dukan su sun godewa Sanata Shehu Sani bisa tona asirin majalisar da yayi a cikin fira da suka yi da majiyar mu.

Naira 13.5 miliyan: Manyan yan gwagwarmaya, gawurtattun lauyoyi sun yi kaca-kaca da majalisar dattijai
Naira 13.5 miliyan: Manyan yan gwagwarmaya, gawurtattun lauyoyi sun yi kaca-kaca da majalisar dattijai

KU KARANTA: Yadda Gwamna Bindow ya taimaka wajen mutuwar mahaifin mu - Iyalan Sale Michika

Legit.ng dai ta samu a baya cewa majalisar dattijan Najeriya a jiya ta tabbatar da ikirarin da Sanata Shehu Sani yayi wanda ke wakilatar mazabar shiyyar Kaduna ta tsakiya daga jam'iyyar APC na cewa kowane Sanata na karbar Naira 13.5 miliyan a matsayin kudin gudanarwa duk wata.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun 'yan majalisar Sanata Aliyu Sabi Abdullahi daga jihar Neja ya fitar inda ya ke tabbatar da batun sannan ya kuma ce shi Sanata Shehu Sani din bai fadi wani sabon abu ba.

Sanata Sabi ya kuma karyata cewa wai 'yan majalisun sun ji haushin Sanata Sani din don ya fadi hakan a wata firar da yayi da manema labarai.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel