An sake ceto wasu 'yan Najeriya su 50 daga Sahara zasu gudu Turai

An sake ceto wasu 'yan Najeriya su 50 daga Sahara zasu gudu Turai

- Mutane a kalla 50 ne ‘Yan gudun hijira daga Najeriya aka ceto a cikin mutane daruruwa da jami’an tsaro na kasar Libiya suka ceto daga cikin Teku.

- ‘Yan Najeriyar na cikin Jirgin Ruwa ne tare da wasu mutun 110 masu hijira. An cetosu ne da wani Jirgin ruwa mai lakabin Aquarius, wanda hukumar Likitoci marasa iyakar aiki (MSF), ke amfani dash

- Fiye da rabin ‘yan hijirar ‘yan Najeriya ne wanda 18 a ciki mata ne sai yaro daya, sauran kuma daga kasashen kusa da sahara suku, sai mutne biyu ‘yan kasar Palastin ne

An sake ceto wasu 'yan Najeriya su 50 daga Sahara zasu gudu Turai

An sake ceto wasu 'yan Najeriya su 50 daga Sahara zasu gudu Turai

Mutane a kalla 50 ne ‘yan gudun hijira daga Najeriya aka ceto daga cikin daruruwan mutane dajamia’n tsaro na kasar Libiya da kuma kungiyar agaji ta kasa da kasa suka ceto daga cikin Teku.

‘Yan Najeriyar na cikin Jirgin Ruwan ne tare da wasu mutum 110 masu hijira. An ceto ne da wani Jirgin Ruwa mai lakabin Aquarius, wanda hukumar Likitoci marasa iyakar aiki (MSF), ke amfani dashi, mil 21 daga Yammacin yankin. Jirgin zai kai ‘Yan gudun hijirar ne zuwa kasar Italiya, wanda suka hada da mata 18 sai yaro daya.

DUBA WANNAN: PDP ta maida martani kan batun juyin mulki

Majiyar Legit.ng ta bayyana cewa fiye da rabin mutanen dake cikin Jirgin Ruwan ‘yan Najeiya ne, sauran kuma daga kasashen kusa da sahara sai mutum biyu ‘yan kasar Palastin.

Jami’an tsaro na kasar Libiya sun jajirce wurin tare Jiragen ruwa na ‘yan gudun hijira kafin su kaiga isa tashar manyan minyan Jirage na duniya da zasu shigar dasu Turai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel