Wata sabuwa: Sabbin malaman makarantar da aka dauka a Kaduna sun kasa rubuta wasikar turanci

Wata sabuwa: Sabbin malaman makarantar da aka dauka a Kaduna sun kasa rubuta wasikar turanci

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya bayyana takaicin sa game da yadda yace wasu daga cikin sabbin malaman makarantar da aka jihar ta dauka aiki a kwanan baya sun kasa rubuta sahihiyar wasikar turanci ta amincewa da karbar aikin da aka basu.

Gwamnan dai ya kwarmata hakan ne a wani sako da ya rubuta a shafin sa na dandalin sada zumunta a ranar Alhamis 8 ga watan Maris din wannan shikerar.

Wata sabuwa: Sabbin malaman makarantar da aka dauka a Kaduna sun kasa rubuta wasikar turanci
Wata sabuwa: Sabbin malaman makarantar da aka dauka a Kaduna sun kasa rubuta wasikar turanci

KU KARANTA: Kotu tace a kamo mata wani sanatan APC

Legit.ng dai ta tuna cewa gwamnan jihar a watannin baya ya sha suka daga bangarori da dama na kasar nan bisa korar ma'aikata sama da dubu 20 da yayi sakamakon faduwa jarabawar da suka yi a jihar.

A wani labarin kuma, Jiragen alfarma na shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari guda biyu da yayi alkawarin sayarwa domin tattalin kudin kasa na Falcon 7X da kuma Hawker 4000 har yanzu suna nan, kamar dai yadda binciken wata majiyar mu ta tabbatar.

Sai dai kamar yadda muke samu, fadar shugaban kasar ta bayyana cewa masu sayen jiragen ne suka yi masu tayin banza shine ma kuma babban dalilin da yasa har yanzu ba a saida su ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng