Shugaba Buhari ya kaddamar da shirin tallafin kayan gona a jihar Flato

Shugaba Buhari ya kaddamar da shirin tallafin kayan gona a jihar Flato

Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabuwar shirin tallafawa manoma da tarakta domin saukaka aikin noma domin cigaban da farfado da tattalin arzikin kasa.

Shugaban kasan ya kaddamar da wannan shiri ne a yau Juma’a, 9 ga watan Maris, 2018 a garin Jos, babban birnin jihar Plateau.

Jaridar Legit.ng ta kawo muku cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya isa filin jirgin saman Yakubu Gowon da ke garin Heipang jihar Flato misalin karfe 11:50 na safiyar Alhamis, 8 ga watan Maris, 2018.

Shugaba Buhari ya kaddamar da shirin tallafin kayan gona a jihar Flato
Shugaba Buhari ya kaddamar da shirin tallafin kayan gona a jihar Flato

Gwamnan jihar, Simon Lalong, tare da tsaffin gwamnonin jihar 2 kuma sanatoci a yanzu, Joshua Dariye da Jonah Jang; ministan wasanni, Solomon Dalung, tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar, Pauline Tallen da sauran su ne suka tarbesa a filin jirgin sama.

Shugaba Buhari ya kaddamar da shirin tallafin kayan gona a jihar Flato
Shugaba Buhari ya kaddamar da shirin tallafin kayan gona a jihar Flato

Ana sa ran shugaba Buhari zai kaddamar da wasu hanyoyi da gwamnan ya gina irinsu Mararaban Jama'a- Secretariat junction-British America junction road, Miango-Wild Life Park-Rafiki junction, Domkat Bali/Tudun Wada/old airport roundabout township roads da sauransu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng