Babban Shehin yan Shi’a ya kwance masu zani a kasuwa
Rahotanni sun kawo cewa babban Shehin Musulmai mabiya Shi’a, Kamal Al Haidari ya yayewa mabiyansa zani a kasuwa, inda ya bayyana cewa mafi akasarin hadisansu Kirista, Majusawa da Yahudawa ne suka rawaito su.
Shugaban kungiyar na asali, ya furta wannan kalamin a yayin wani shirin talabiji, inda ya ce :
"Mafi akasarin hadisan mabiya Shi'a Rafidha, Kirista, Majusawa da Yahudawa suka rawaito su, a ciki har da littafin tafsiri na AL Qomi wanda ya kasance daya daga cikin sanannun litattafai.
"Wadannan litattafan na kunshe da karyace-karyace, kwaskwarima,kazafi da aika-aika marasa misaltuwa, duk da Malam Al Khoei ya nemi tsaftace su.
KU KARANTA KUMA: Harin bom – Kotu ta yanke wa Charles Okah hukuncin daurin rai da rai
"Kowa ya san da haka, amma wasu jahilan malamai masu sanye da bakeken alkyabbobi ke ci gaba da rufe ido don yin amfani da su a wajen batar da jama'a".
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng