Kamfanin Coke zai fara sayar da barasa a fadin duniya

Kamfanin Coke zai fara sayar da barasa a fadin duniya

- Kamfanin Coca Kola yana lemo ne kawai da ruwansa a da

- YAnzu yace shima zai fara sayar da giya

- Sai dai ba'a san ko a tulu daya za'a hada ba

Kamfanin Coke zai fara sayar da barasa a fadin duniya
Kamfanin Coke zai fara sayar da barasa a fadin duniya

Tun da aka kafa kamfanin Coka-Kola dai, shekaru 125 da suka wuce, bai taba yin giya ba, a manyan kamfanunuwansa da store da depo da suka kai kamar 10,000 a fadin duniya, sai a wannan karo kamfanin yace zai fara sayar da giya saboda ribar yin hakan.

Abida dai biliyoyin mashaya zasu so ji tukun, shine ko dai ta yaya za'a faro shirin, ko tulunan da aka yi lemin ne za-kuma a dura kayan giya a ciki, ko kuwa za'a surka a dauraye ko a canja. Wannan na zuwa ne lokacin da mutane kan kokarin kaucwa giya saboda kiwata hanta.

DUBA WANNAN: Yadda aka saci 'yan matan Dapchi a Yobe

A dai inda za'a fara wannan aiki, kamar yadda BBC ta ruwaito, watau a kasar Jampan, a cikin lemon kwalbar ne ma za'a diga giyar, kamar kashi biyu cikin goma, wai don qarin dadi da kuma samun riba dama auki.

Ko hakan zai faru a kasashen musulmi, oho, sai ku biyo mu, mu kuma muna kasa muku kunne.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel