Ya kamata gwamnatin tarayya ta saka dokar ta baci a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa - Edwin Clark

Ya kamata gwamnatin tarayya ta saka dokar ta baci a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa - Edwin Clark

- Cif Edwin Clark yayi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya saka dokar ta baci a jihohin Borno, Yobe da Adamawa.

- Ya ce saka dokar ta bacin wajibi ne, domin bawa sojoji damar gabatar da aikin su yanda ya kamata.

- Ya zargi Gwamnonin jihohin Borno, Yobe, da Adamawa da kokarin tadawa gwamnatin tarayya hankali

Ya kamata gwamnatin tarayya ta saka dokar ta baci a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa - Edwin Clark
Ya kamata gwamnatin tarayya ta saka dokar ta baci a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa - Edwin Clark

Tsohon Ministan labarai, Cif Edwin Clark yayi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya saka dokar ta baci a jihohin Borno, Yobe da Adamawa. Ta ce, yayi kiran ne saboda ganin matsalar hare-haren ta'addancin da kuma rashin tsaro a jihohin.

DUBA WANNAN: Kotu ta bawa Hukumar EFCC umarnin kama shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai , Mista Ogor

Cif Clark ya bayyana cewa saka dokar ta bacin wajibi ne, domin bawa sojoji damar gabatar da aikin su yanda ya kamata. A cikin wata wasika da ya aikawa babban ministan shari'a, Abubakar Malami, wanda aka karantawa manema labarai a gidan shi dake Abuja jiya, Clark ya roki Malami akan ya cigaba da kokari, sannan kuma ya umarci sojoji su kawo karshen tashin hankalin da ake fama dashi a yankunan a cikin watanni shida.

Tsohon ministan ya ce, sace 'yan matan makarantar Dapchi 110 da aka yi a jihar yobe, hakan na nuna cewa 'yan ta'addan Boko Haram din suna nan da karfin su a yankin, sannan kuma barin su zai sa su cigaba da tada hankalin al'ummar yankin.

Sannan ya zargi Gwamnonin jihohin Borno Kashim Shettima, Yobe Ibrahim Geidam, da Adamawa Jibrila Bindow, da kokarin tada wa gwamnatin tarayya hankali duk da irin kokarin da take na ganin ta magance hare-haren da ake yi a jihohin su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel