Kasar Saudiyya ta bayar da tallafin miliyan $10, kayan agaji ga Najeriya

Kasar Saudiyya ta bayar da tallafin miliyan $10, kayan agaji ga Najeriya

- Kasar Saudiyya ta bayar da tallafin kudi, miliyan $10, da kayan agaji ga Najeriya

- Ministan tsaro, Mansur Dan-Ali, ya karbi kyautar a madadin gwamnatin tarayya daga hannun wakilan gwamnatin kasar Saudiyya

- Kasar Saudiyya ta ce ta bayar da tallafin ne domin taimakon mutanen dake sansanin 'yan gudun hijira a jihohin da aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram ya fi shafa

A yau ne tawagar wakilan gwamnatin Saudiyya su ka isa ma'aikatar tsaro ta Najeriya domin bayar da agajin kudi da kayan aiki ga gwamnatin Najeriya.

Shugaban tawagar, Nasir Bin Mutlak, ya bayyana cewar sun bayar da agajin ne domin taimakon mutanen dake sansanin 'yan gudun hijira a jihohin da aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram ya fi shafa a yankin arewa maso gabas.

Kasar Saudiyya ta bayar da tallafin miliyan $10, kayan agaji ga Najeriya

Buhari da Sarki Salman na Saudiyya

Ministan tsaro Mansur Dan-Ali be ya karbi tallafin a madadin gwamnatin tarayya a ma'aikatar tsaro.

Kasar Saudiyya ta bayar da tallafin kudi, miliyan $10 da kayan agaji da su ka hada da kayan amfanin sojoji.

A jawabin sa, jagoran tawagar, Mutlak, ya ce "Dala miliyan goma ($10m) tallafin ne daga cibiyar aikin agaji da Jin kai ta sarki Salman dake Saudi. Mun kawo wannan agaji ne domin nuna tausayin mu ga halin da mutanen dake sansanin 'yan gudun hijira su ka tsinci kan su da kuma nuna kyamar mu ga aiyukan ta'addanci."

DUBA WANNAN: Ya yi ikirarin Allah ne ya aiko shi saboda irin mu'ujizar da yake nunawa

Mutlak ya ce tawagar sa zata kai ziyara yankin arewa maso gabas domin ganin sanin wurin da aka fi bukatar taimako.

Da yake jawabi, Ministan tsaro Mansur Dan-Ali, ya yi godiya ga gwamnatin kasar Saudi bisa wannan gagarumar gudunmawa tare da shaidawa tawagar cewar tallafin da su ka bayar zai matukar tallafawa wajen sayen kayan aikin yaki da ta'addanci ga hukumar sojin Najeriya.

Dan-Ali ya kara da cewar taimakon ba iya na Najeriya bane domin akwai 'yan kasar Nijar, Chad, da Kamaru, a sansanin 'yan gudun hijirar Najeriya.

Ragowar 'yan tawagar sun hada da; Kahlid Bin Abdulrahman Al-Mani da Muhammad Bin Addidat Al-Namla.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel