Al-Qur'ani shine babban Kundi mai koyar da zaman Lafiya - Buhari

Al-Qur'ani shine babban Kundi mai koyar da zaman Lafiya - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi nema tare da gargadin 'yan Najeriya akan yin riko da fahimtar dukkanin littafai da Allah Madaukakin Sarki ya saukar wajen fadakarwa tare da wa'azantar da zaman lafiya a tsakankanin al'umma.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a jihar Katsina, yayin biki na rufe taron gasar karatun Al-Qur'ani ta kasa da aka gudanar karo na 32 a ranar Asabar din da ta gabata.

Shugaba Buhari yake cewa, ko shakka babu Al-Qur'ani shine babban kundin tsari da ya kunshi duk wani tafarki na rayuwar bil Adama. Kuma littafin Mai Girma ya koyar damu yadda zamu yi gaskiya da kuma adalci a duk mu'amalan mu da ya hadar har wadanda ba musulmai ba.

Shugaba Buhari tare da Sheikh Bala Lau
Shugaba Buhari tare da Sheikh Bala Lau

Ya ci gaba da cewa, "tarihin rayuwar Manzo kuma Annabin mu Muhammadu Sallalahu Alaihi Wassalama ya bayyana cewa, akwai wani lokaci da aka tsananta wa Musulmai, inda suka koma wata Daula ta kafirai a kasar Habasha kuma suka zauna lafiya tare da aminci".

KARANTA KUMA: IBB da Danjuma sun shiga ganawar sirrance a birnin Minna

Legit.ng ta fahimci cewa, karamin ministan sufuri na jiragen sama, Hadi Sirika, shine ya wakilci shugaba Buhari a wannan taro.

Ya kara da cewa, ya kamata mu riki Al-Qur'ani a matsayin madubin haskaka rayuwar mu ba abin kawata gidajen mu ba.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, ajali ya riski wani matashi saman itacen Kwakwa a jihar Imo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng