Nigerian news All categories All tags
'Yin ciki da haihuwa na tsofar da mace da wuri, qarin shekaru 11 kan shekarunta'

'Yin ciki da haihuwa na tsofar da mace da wuri, qarin shekaru 11 kan shekarunta'

- Ciki da haihuwa na tsofar da mace da wuri

- A kowanne ciki an qiyasta kamar tana qarin shekaru 11 ne ga jikinta

- Mata da yawa a kasashen Turai basu son haihuwa

'Yin ciki da haihuwa na tsofar da mace da wuri, qarin shekaru 11 kan shekarunta'

'Yin ciki da haihuwa na tsofar da mace da wuri, qarin shekaru 11 kan shekarunta'

Sabon bincike kan kwayoyin halitta da masana suka yi, ya nuna cewa DNA na tsofewa da shekaru 11 ga duk macen da tayi ciki kuma ta haifeshi.

Wannan na nufi duk wadda tayi 'ya'ya uku ta qara shekaru 33 ne kan kwayoyin halittarta, inji sabon binciken.

Daukar cikin na rage tsahon telomere ne, wanda shi yake kife bakunan shi sinadarin na DNA, wanda hakan kan zamewa jikin mace wani naqasu, wanda masanan suka ce ya fi na qiba da na shan sigari illa ga jikin matan.

DUBA WANNAN: APC tace Buhari ne dan takarar ta a 2019

Study author Dr. Anna Pollack from George Mason University, Virginia, United States (U.S.), wadda ita ta wallafa binciken a kasar Amurka, tace hakan ya basu mamaki, inda suka danganta wannan sabon ilimi kan wahalar da matan kansha daga daukar ciki da rainonsa, wanda ke tsofar da kwayoyin halittarsu matan da wuri.

A can dai kasashen Turai, an ma daina haihuwa barkatai, inda wasu kan gwammace ma su zauna babu aure, sai dai saduwa kawai don jin dadinsu, wasu kuwa sukan yi 'ya'ya biyu ko daya kacal.

Yawanci aiki ne dai da bukatar samun damar yin wasu abubuwa na rayuka kan hana su lokacin haihuwa. Su kuwa mata a kasashen Afirka, Latin Amurka da Asiya, kan haihi yara kamar 7-12 a tsakanin shekaru 20.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel