Da dumin sa: Kamfanin NNPC ya amince ya gina sabuwar matatar mai a wannan jihar ta Arewa
Sahihan bayanan da muke samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa rukunin kamfanonin nan mallakin gwamnatin tarayya dake kula da albarkatun man fetur watau Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) sun shiga yarjejeniya da gwamnatin jihar Kogi da zummar kafa matatar mai ta zamani watau biofuel plant a turance.
Kamar yadda muka samu, tuni har an kammala saka hannu akan takardar yarjejeniyar a garin Abuja, jiya Talata inda ake sa ran matatar man zata rika samar da mai domin ababen hawa nan ba da dadewa ba.
KU KARANTA: Sojoji sun kama makiyaya a Adamawa
Legit.ng haka zalika ta samu cewa gwamnan jihar Yahaya Bello da yayi tsokaci jim kadan bayan saka hannu a takardar yarjejeniyar ta bayyana cewa matar man za ta samar da ayyukan yi ga dubban matasan jihar.
Haka ma dai Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta sanar da zuwa karshen watan Satumba na wannan shekarar a matsayin lokacin da za ta fara biyan sabon tsarin albashi ga ma'aikatan ta a dukkan fadin kasar nan.
Wannan dai kamar yadda muka samu na kunshe ne a cikin bayanin maraba da babban ministan kwadago da samar da aikin yi na kasar Sanata Chris Ngige ya yi jiya Litinin lokacin da yake jawabi a lokacin bikin cikar kungiyar kwadago ta kasa shekara arba'in da kafuwa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng