Sanata Abdullahi Adamu ya bukaci masu yiwa gwamnatin Shugaba Buhari zagon kasa dasu fice daga jam'iyyar APC

Sanata Abdullahi Adamu ya bukaci masu yiwa gwamnatin Shugaba Buhari zagon kasa dasu fice daga jam'iyyar APC

- Wani Sanata ya bukaci masu yiwa gwamnatin shugaba Buhari zagon kasa da su fita daga jam'iyya APC din

- Ya yi wannan kiran ne a jihar Nasarawa a wata zantawa da yayi da 'yan jam'iyyar

- Ya ce abin kunya ne ace wasu kawai kokarin da suke shine suga gazawar shugaban Kasar

Sanata Abdullahi Adamu ya bukaci masu yiwa gwamnatin Shugaba Buhari zagon kasa dasu fice daga jam'iyyar APC
Sanata Abdullahi Adamu ya bukaci masu yiwa gwamnatin Shugaba Buhari zagon kasa dasu fice daga jam'iyyar APC

Daya daga cikin 'yan majalisar Dattijan kasar nan ya zargi wasu daga cikin abokan aikin sa tare da wasu daga cikin 'yan majalisar wakilan jiha bisa nuna rashin goyon baya da kuma zagon kasa da suke yi wa shugaba Buhari. Inda ya bukaci duk su fita su bar jam'iyyar.

DUBA WANNAN: Kwallon Kwando: Najeriya na gab da shiga gasar duniya

Sanatan ya ce bai ga ma'anar amfani da jam'iyya ba aci zabe kuma azo daga baya ana zubar mata da mutunci, yayi wannan jawabi ne a jihar Nasarawa, inda ya zanta da 'yan jam'iyyar ya kuma yi Allah wadai ga wasu daga cikin 'yan majalisar masu yiwa gwamnatin shugaba Buharin zagon kasa.

A makon da ya wuce ne aka cire tsohon gwamnan jihar Nasarawan daga cikin kwamitin majalisar Dattawa na yankin Arewa.

Ya kara da cewa, yin zagon kasa ga Gwamnatin shugaba Buhari ga dan majalisar tarayya ko na jiha, kamar yiwa dokar kasa butulci ne. Ya ce ba abun damuwa bane idan dan jam'iyyar PDP yayi hakan saboda dama shi dan adawa ne.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel