Dandalin Kannywood: Harkar fim ta fi rayuwar jami'a wahala - Halima Ibrahim

Dandalin Kannywood: Harkar fim ta fi rayuwar jami'a wahala - Halima Ibrahim

- Harkar fim ta fi rayuwar jami'a wahala - Halima Ibrahim

- Ta kuma siffanta masana'antar da wata makaranta dake cike da darussa

- Ta ce ta koyi hakuri tare da zama da mutane

Daya daga cikin sabbin fuskoki a masana'antar shirya fina-finan Hausa da ake yi wa lakani da Kannywood da ke da hedikwatar ta a garin Kano mai suna Halima Ibrahim ta siffanta masana'antar da wata makaranta dake cike da darussa da dama.

Dandalin Kannywood: Harkar fim ta fi rayuwar jami'a wahala - Halima Ibrahim
Dandalin Kannywood: Harkar fim ta fi rayuwar jami'a wahala - Halima Ibrahim

KU KARANTA: Muna so muyi aure lokaci daya - Gimbiya da Sa'a na Dadin Kowa

Haka zalika jarumar ta kara da siffanta harkar fina-finan da cewa ta fi ta rayuwar jami'a wahala ta ko wane bangare musamman ma dai yadda mutum zai yi gogayya da jaruman da suka kware kuma duniya ta san su.

Jarumar dai ta yi wannin kalamin ne yayin da take zantawa da majiyar mu ta mujallar Fim inda ta bayyana cewa ita ma tabbas ta koyi darussa da dama tun daga shigar ta masana'antar tare kuma da sauran ilimin zaman rayuwa.

Legit.ng ta samu cewa jarumar ta kara da cewa shigowar ta masana'antar ta sa yanzu ta koyi hakuri tare da zama da mutane kasantuwar yanzu ta kan yi mu'amala da jama'a da dama kuma daga fannonin rayuwa iri daban-daban.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng