Gobara ta tashi a sansanin yan gudun hijira dake jihar Filato
Wata gobara ta tashi a sabon sansanin yan gudun hijira da gwamnatin taraya ta gina a karamar hukumar Shendam, jihar Filato, a ranar Talata, 20 ga watan Feburairu, inji rahoton Sahara Reporters.
Wata Kwamitin gwamnatin tarayya dake kula da yan gudun hijira ne ta samar da wannan sansani, tun bayan matsalar ambaliyan da aka samu a shekarar 2012 da ta shafi jihohi 24 na kasar nan.
KU KARANTA: Buhari ya fada ma gwamnoni su saurara masa game da tsayawa takarar shugaban kasa a 2019
Wani Darakta a hukumar bada agajin gaggawa na jihar Filato, Bintan Wuyep ya tabbatar da rahoton ga majiyar Legit.ng, inda yace har yanzu hukumarsu bata tantance matsayin asarar da aka tafka a sakamakon gobarar ba.
“Ko kudin mai da zamu sanya ma motar da zata kai mu sansanin bamu da shi, mun nemi kudi mun rasa, ko bashi ba’a bamu, don haka bamu san matsayin barnar da gobarar da tayo ba, don bamu je ba, sakamakon rashin mai a motocin mu na aiki.” Inji Wuyep.
Daga karshe Wuyep ya bayyana gobarar a matsayin babban rashi ga Najeriya da jihar Filato, sa’annan ya bukaci gwamnatin jihar ta taimaka musu da kudade don gudanar da ayyukansu yadda suka kamata. Haka zalika yay aba ma majalisar dokokin jihar da ta yi alwashin binciken musabbabin gobarar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng