Zaben 2019: Wasu manyan 'yan Najeriya na son Tambuwal ya ya kalubalanci Buhari
Rahotanni sahihai da muke samu daga majiyoyin mu dai na nuni da cewa yanzu haka Gwamnan jihar Sokoto da kuma ke zaman tsohon kakakin majalisar wakillan Najeriya watau Alhaji Aminu Waziri Tambuwal na fuskantar matsin lamba daga manyan 'yan siyasar kasar nan.
Mun samu dai cewa matsin lambar dai na da nasaba dason da suke yi masa ya fito ya kalubalanci shugaba Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa.

KU KARANTA: Malamin addini ya shawarci Buhari ya jingine batun takara a 2019
Haka ma dai mun samu cewa manya daga cikin yan siyasar Najeriya dake a jam'iyyar PDP a mataki na kasa na ta jawarcin tsohon kakakin majalisar don ganin ya dawo jam'iyyar sa ta PDP.
Legit.ng ta samu cewa hujjojin da ake bayarwa game da hakan shine ganin gwamnan na Sokoto yana da kananan shekaru sannan kuma yana da kwarewa ta fannonin rayuwa da mulki da kuma ilimi musamman ma kuma ganin ya fito ne daga yanki daya da shugaba Buhari din na arewa maso yammacin Najeriya.
A wani labari kuma, Wani babban malamin addinin kirista kuma dan siyasa dake zaman shugaba na kasa gaba daya na jam'iyyar adawa ta Democratic People’s Congress (DPC) a takaice mai sun Rabaran Olusegun Peters ya gargadi shugaba Buhari game da sake tsayawa takara a zaben 2019.
Shugaban jam'iyyar ta Democratic People’s Congress (DPC) dai ya kuma ce inda shugaban Muhammadu Buhari yana son talaka da kuma kasar kamar yadda yake ta cewa to dole ne ya janye batun sake yin takarar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng