Allah ya tsare: Daliban makarantar kwana sun tserewa harin 'yan Boko Haram a Yobe

Allah ya tsare: Daliban makarantar kwana sun tserewa harin 'yan Boko Haram a Yobe

- Daliban makarantar kwana sun tserewa harin 'yan Boko Haram a Yobe

- Yan Boko Haram ne dai cike da motocin akori kura su ka je makarantar kwanan da ke garin Dapchi

Rahotannin da muke samu mai dadi dai shi ne wasu dalibai 'yan mata dake a makarantar kwana tare da malamansu sun samu nasarar kubucema wani harin da mayakan kungiyar nan ta Boko Haram su ka kai masu a makarantar su dake a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

KU KARANTA: Yan Boko Haram sun kai sabon hari jami'ar Maiduguri

Kamar dai yadda muka samu, wadanda lamarin ya auku a kan idon su sun ce a jiya ne dai wani ayarin yan bindigar kungiyar ta Boko Haram ne cike da motocin akori kura su ka je makarantar kwanan da ke garin Dapchi ta jihar Yobe.

Legit.ng haka zalika ta tabbatar da cewa zuwa 'yan Boko Haram din ke da wuya sai suka yi ta harbe-harbe sannan kuma suna ta tayar da bama-bamai a makarantar, lamarin da ya sa daliban da malaman tserewa daga makarantar.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a shekarun baya ma dai 'yan kungiyar ta Boko Haram sun samu nasarar sace wasu dalibai mata 'yan makarantar kwana dake a garin Chibok ta jihar Borno, lamarin da yayi matukar daukar hankalin duniya baki day.

A shekarar 2016 ne dai wani sabon bincike ya gano cewa har yanzu babu cikakken tsaro a makarantu a wasu jihohi dake arewa maso gabashin Najeriya, fiye da shekaru biyu bayan sace 'yan matan Chibok.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel