So hana ganin laifi: Hamshakin mai kudi ya zama Kirista sannan ya auri diyar Osinbajo
- Hamshakin mai kudi ya zama Kirista sannan ya auri diyar Osinbajo
- Diyar mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo mai suna Oluwadamilola Osinbajo
- Yanzu kuma an gano cewa Kirista ne da yake aiki a cocin Redeemed Christian Church of God
Sabbin bayanai masu daure kai na cigaba da bayyana a zagaye da auren nan da ake sa ran daurawa a tsakanin diyar mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo mai suna Oluwadamilola Osinbajo ko kuma Kiki da angon ta mai suna Oluseun Bakare da ke zama da ga hamshakiyar mai kudin na Bola Shagaya.
KU KARANTA: 'Yan majalisa su shirya wa Buhari gadar zare a 2019
Kamar yadda muke samu daga majiyoyin mu, a sabanin yadda labarin ya fara fita na cewa wanda zai aure diyar ta Osinbajo musulmi ne, yanzu kuma an gano cewa Kirista ne da yake aiki a cocin Redeemed Christian Church of God.
Legit.ng ta samu cewa ma'auratan ma sun hadu ne a majami'ar wajen ibada kafin daga bisanin soyayya mai karfi ta shiga tsakanin su kuma har ma maganar aure ta shiga.
Wannan ne ma ya sanya mutane da dama ke ganin cewa wanda ke shirin angwancewar musulmi ne a da kafin daga baya a zama Kirista har kuma ma ta amince ta aure shi.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng