Jahohi 11 sun sake karbar bashin Naira 16.1 biliyan daga shugaba Buhari
- Jahohi 11 sun sake karbar bashin Naira 16.1 biliyan daga shugaba Buhari
- Mai taimakawa mataimakin shugaban kasa na musamman ya bayyana hakan
- Mista Akande bai lissafa sunayen jahohin da suka anfana da kudaden ba
Akalla jahohi sha daya daga cikin ashirin da ukku ne da a baya gwamnatin tarayya ta ba lamunin karbar tallafin bashi domin inganta kasafin kudin su sun anshi zunzurutun kudaden da suka kai Naira biliyan 16.1 zuwa watan Janairun shekarar nan da ya gabata.
KU KARANTA: Majalisar tarayya ta shiryawa Buhari gadar zare a 2019
Wannan dai na kun she ne a cikin wata sanarwa da mai taimakawa mataimakin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai watau Laolu Akande ya fitar dauke da sa hannun sa ya kuma rabawa manema labarai.
Legit.ng dai ta samu cewa a cikin sanarwar da ya fitar, Mista Akande bai lissafa sunayen jahohin da suka anfana da kudaden ba amma ya tabbatar da cewa sauran jahohin 12 suma za su karbi kason su nan ba da dadewa ba.
A wani labarin kuma, Majalisar tattalin arziki ta kasa baki daya watau National Economic Council (NEC) a turance a jiya ta baiwa wani kwamitin ta umurnin yin hadin gwiwa da kamfanin samar da albarkatun man fetur na kasa da nufin bullo da wata hanya domin yin gyara ga farashin man fetur.
Gwamnan jihar Bauchi dake a yankin arewa maso gabashin Najeriya, Mohammed Abubakar ne ya sanar da hakan yayin da yake tattaunawa da manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala yin taro da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a jiya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng