Soyayya ta yi tsami: Wani saurayi ya bankawa gidan budurwar sa wuta

Soyayya ta yi tsami: Wani saurayi ya bankawa gidan budurwar sa wuta

- Wani saurayi ya bankawa gidan budurwar sa wuta

- Mun samu dai cewa sai dai shi wanda ake karar ya musanta zargin da ake yi masa

- An bada belin sa kan kudi Naira dubu 150 sannan kuma ya dage shari'ar zuwa ranar 5 ga wata mai kamawa

Wani saurayi mai akalla shekaru 27 a duniya mai suna Ifeanyi Ede a yau dinnan Alhamis ya gurfana a gaban alkalin wata kotun Majistare mai daraja ta daya a garin Abuja bisa zargin sa da ake yi na cinnawa gidan budurwar sa wuta.

Soyayya ta yi tsami: Wani saurayi ya bankawa gidan budurwar sa wuta
Soyayya ta yi tsami: Wani saurayi ya bankawa gidan budurwar sa wuta

KU KARANTA: Tsohon kwamishinan Abiya ya koma APC

Dan sanda mai gabatar da kara mai suna Idowu Lawal kamar yadda muka samu tun farko ya bayyanawa kotun cewa shi dai wanda yake tuhumar ya bankawa gidan budurwar sa mai suna Esther Yahaya dake zaune a garin Kubwa, Abuja wuta a ranar 5 ga watan nan da muke ciki.

Legit.ng ta samu dai cewa sai dai shi wanda ake karar ya musanta zargin da ake yi masa kafin daga bisani alkalin kotun ya bada belin sa kan kudi Naira dubu 150 sannan kuma ya dage shari'ar zuwa ranar 5 ga wata mai kamawa.

Kuma a dayan bangaren Wani mummunan labarin da ke iske mu daga majiyar mu na bayyana cewa akalla rayuka 150 ne kawo yanzu suka salwanta sannan kuma wasu 556 suka jikkata a sakamakon hadduran ababen hawa 170 da suka auku a jihar Jigawa cikin shekarar da ta gabata ta 2017.

Shugaban hukumar nan ta dogarawan hanya mallakin gwamnatin tarayya na shiyyar jihar mai suna Angus Ibezim shine ya sanar wa da manema labarai hakan a yayin firar da yayi da su a ofishin sa dake a garin Dutse, babban birnin jihar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng