Badakalar $44m na hukumar NIA: Majalisar wakilai ta titsiye Kingibe a sirrance
A ranar Talatar da ta gabata ne, majalisar wakilai ta titsiye shugaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa akan binciken hukumar NIA, Ambasada Babagana Kingibe, a sirrance.
Aminu Sani Jaji na jam'iyyar APC, shine jagoran wannan kwamiti na binciken yadda dala miliyan 44 suka yi layar bata daga asusun hukumar NIA da kuma cancantar sabon shugaban ta, Ahmed Rufa'i Abubakar.
A makon da ya gabata ne, wannan kwamiti ya yiwa Kingibe kiranye da wasu mambobin kwamitin sa bayan bai amsa goron gayyatar su a karo na baya.
KARANTA KUMA: Hotunan ganawar shugaba Buhari da tsohon shugaba Abdulsalami
Legit.ng ta fahimci cewa, Kingibe ya gana da majalisar ta wakilai na tsawon awanni biyu a sirrance, inda yace ba zai bayar da wani jawabi ba muddin 'yan jarida na farfajiyar majalisar.
Jaridar ta kuma ruwaito cewa, matar wani dan majalisar dokoki ta jihar Katsina, ta sheka lahira a yayin da ta sha wani tsimi domin samun yalwar ruwan mama da zai wadatar da jariran ta tagwaye.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng