Dandalin Kannywood: Na fara shiga matsaloli bayan na fara yin fina-finan kudu - Rahma Sadau

Dandalin Kannywood: Na fara shiga matsaloli bayan na fara yin fina-finan kudu - Rahma Sadau

- Na fara shiga matsaloli bayan na fara yin fina-finan kudu - Rahma Sadau

- Jarumar tace ta na shan bakar ukuba daga 'yan uwan sana'ar ta na Kannywood

- Jarumar dai an dakatar da ita daga fina-finan Hausa a shekarar 2016

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood watau Rahama Sadau, ta bayyana a ranar Asabar din da ta gabata cewar, ta soma shiga matsalolin rayuwa ne tun bayan da ta fara fitowa a shire-shiren fina-finan kudancin kasar nan ta Najeriya da aka fi sani da Nollywood.

Dandalin Kannywood: Na fara shiga matsaloli bayan na fara yin fina-finan kudu - Rahma Sadau
Dandalin Kannywood: Na fara shiga matsaloli bayan na fara yin fina-finan kudu - Rahma Sadau

KU KARANTA: Yan sanda sun kama gaggan barayi da likita ke shugabanta

Jarumar dai wadda aka dakatar da ita daga fina-finan Hausa a shekarar 2016 ta bayyana yadda tace ta na shan bakar ukuba daga 'yan uwan sana'ar ta na watau jaruman masana'antar Kannywood.

Legit.ng ta samu dai cewa jarumar ta kuma ce tabbas ba abu ne mai dadi ba kwata-kwata yadda ta ke shan tsangwama a wasu lokuttan idan mutun ya tsallaka zuwa shirin finafinai na kudanci ko na turawa musamman ma don dai yadda al’adu da dabi’u suka banbanta kawai.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa har yanzu dai jarumar na cikin dambarwa da jiran tsammani tun bayan dawowar ta daga kasar Turkiyya inda ta shafe akalla watanni uku tana wani karatu yanzu kuma ta dawo gida tana jiran kungiyar su ta masu shirya fina-finan watau MOPPAN ta dake dakatarwar da ta yi mata.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng