Banyi nadamar rabon kaskon suya ga jama'a ta ba - Sanatan Najeriya
- Sanatan Najeriya mai wakiltar jihar Abiya ta arewa, Cif Mao Ohuanbunwa, ya bayyana cewar bai yi nadamar rabon kaskon suya ga jama'ar da suka zabe shi ba
- A kwanakin baya ne Sanata Ohuanbunwa ya yi rabon kaskon suya ga jama'ar mazabar sa a matsayin tallafin sana'o'i
- 'Yan Najeriya sun nuna matukar mamakinsu ga abinda Sanata Ohuanbunwa ya yi
Sanatan Najeriya mai wakiltar jihar Abiya ta arewa, Cif Mao Ohuanbunwa, ya bayyana cewar ko kadan ba ya nadamar rabon kaskon suya da yayi ga jama'ar mazabar sa duk da shakiyanci da yace 'yan Najeriya nayi masa a kan hakan.
A kwanakin baya ne Sanata Ohuanbunwa ya ya yi rabon kaskon suya ga jama'ar mazabar sa a shirinsa na tallafawa matasa domin dogaro da kai.
Sanatan ya bayyana haka ne yayin rufe bayar da tallafi ga matasa karo na biyu a cibiyar koyar da matasa sana'o'i a garin Ohafia dake jihar Abiya.
Sanatan ya bayyana cewar babu wani abin nadama a abin da yayi duk da shakiyancin da wasu 'yan Najeriya ke yi masa, musamman a dandalin sada zumunta da kafafen watsa labarai.
DUBA WANNAN: Zanga-zangar mayar da shugaban hukumar NHIS: 'Yan sanda sun mamaye harabar hukumar
"Bana nadamar rabon kaskon suya ga jama'ar mazaba ta. Masu kira na da "Sanata mai kaskon suya" kamata yayi su kira ni da "Sanata mai bayar da tallafi" domin hakan yafi dacewa. Ba iya kaskon suya na raba ba. Me zaka bawa matar dake sana'ar sayar da kosai da ya wuce kaskon suya?," a cewar Sanata Ohuanbunwa.
"Ba zai bayar da wata ma'ana ba ace kana an bawa direban mota jirgin kasa. Idan kai direban mota ne, mota zan ba ka. Na raba babura masu kafafu uku, kekunan dinki da kayayyaki masu yawa. Saboda haka bana nadama ko damuwa da kira na 'Sanata mai kaskon suya'" a cewar Sanata Ohuanbunwa.
"Na raba tukunyar gas, risho, cokula, har da kudi bayan kaskon suyar", kamar yadda Sanata Ohuanbunwa ya fadi da bakinsa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng