Shugaba Buhari tataccen marar adalci ne - Shugaban jam'iyyar PDP Secondus

Shugaba Buhari tataccen marar adalci ne - Shugaban jam'iyyar PDP Secondus

- Shugaba Buhari tataccen marar adalci ne - Shugaban jam'iyyar PDP Secondus

- Ya yi wannan ikirarin ne a yayin da yake zantawa da wasu 'yan majalisun tarayyar Najeriyar yan PDP

- Ya bukaci dukkan 'yan kasar su taimaka domin kawar da ita a zaben 2019.

Shugaban jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, watau Prince Uche Secondus ya bayyana cewa a halin yanzu 'yan kasar nan na fuskantar wani irin bakin mulki mai cike da son kai da rashin adalci a karkashin shugabancin shugaba Muhammadu Buhari da kuma jam'iyyar All Progressives Congress karara.

Shugaba Buhari tataccen marar adalci ne - Shugaban jam'iyyar PDP Secondus
Shugaba Buhari tataccen marar adalci ne - Shugaban jam'iyyar PDP Secondus

KU KARANTA: Sabon rikici ya yi dalilin salwantar rayuka a Adamawa

Mista Uche Secondus ya yi wannan ikirarin ne a yayin da yake zantawa da wasu 'yan majalisun tarayyar Najeriyar a karkashin inuwar jam'iyyar su a ranar Talatar da ta gabata ne a garin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa hakika wannan mulkin na jam'iyyar APC ba abun da ya kawo wa 'yan Najeriya sai bala'in wahala da ba su taba shiga ba don haka ne ma ya bukaci dukkan 'yan kasar su taimaka domin kawar da ita a zaben 2019.

A wani labarin kuma, Kamar yadda muka samu daga kafar sadarwar zamani ta tuwita, Gwamnan jihar Benue dake a yankin Arewa ta tsakiya watau Gwamna Samuel Ortom ya bayyana cewa yana nan yana nazarin barin jam'iyyar sa ta APC ya zuwa jam'iyyar PDP.

Wannan dai na kunshe ne a wani sakon rubutu da Sanatan nan dake wakiltar mazabar yankin Jihar Bayelsa, Sanata Ben Murray-Bruce ya wallafa a shafin sa na Tuwita inda ya bayyana cewa Gwamnan na jihar Benue ya tabbatar masa da hakan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng