Hotunan ta'aziyyar Gwamna Obaseki ga iyalan direban da 'dan sanda ya kashe a Edo
Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya kai ziyarar ta'aziya ga iyalan direban motar da wani dan sanda ya kashe, abin da ya haifar da tarzoma tsakanin fusatattun matasa a birnin Benin.
Marigayi David Okoniba ya rasu ne sakamakon rashin jituwa da ya faru tsakanin sa da wani jami'in dan Sanda. Gwamnan ya ware kudi N10m domin daukar dawainiyar yara biyu da marigayin ya bari, har ila yau ya kuma ce gwamnati za ta daukin nauyin jana'izan marigayin.
KU KARANTA: Zaben 2019: INEC ta nemi EFCC ta sa ido kan kudaden da 'yan siyasa ke kashewa
Haza zalika, Gwamnan ya kafa kwamiti da za ta gudanar da bincike kan lamarin don zartar da hukuncin da ya dace.
Ga hotunan ziyayar ta'aziyar da gwamnan tare da mukarrabansa suka kai gidan marigayin a kasa.
A baya, Legit.ng ta ruwaito muku yadda fusatattun matasa a jihar ta Edo suka kone wata motar yan sanda sakamakon kashe direban.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng