Dandalin Kannywood: Duk mai zagi na sai na ga bayan sa - Jaruma Ummi Zee-Zee
- Duk mai zagi na sai na ga bayan sa - Jaruma Ummi Zee-Zee
- Ta ce dukkan wanda ya kara zagin ta to kam tabbas zata iya kashe ko nawa ne domin ta sa a kama mata shi
- A bai jarumar ta ce dukkan mai dagewa akan son shugaba Buhari bai san mai ke masa ciwo ba
Mun samu daga majiyar mu ta jaridar Dimokuradiyya dai cewa fitacciyar jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood watau Ummi Zee Zee ta yi kashe di da babbar murya ga dukkan masu zagin ta a kafafen sadarwar zamani.
KU KARANTA: Buhari zai kara kafa sansanin soji a Arewa
Jarumar dai an ruwaito cewar wai ta ambata cewa dukkan wanda ya kara zagin ta to kam tabbas zata iya kashe ko nawa ne domin ta sa a kama mata shi a kuma daure shi a bayan kanta domin ba zata kara lamunta ba.
Legit.ng dai ta samu cewa wannan bai rasa nasaba da irin yadda jama'a suka rika yin tururuwa wajen zagin na ta a kafafen sadarwar zamanin tun bayan da ta fito ta bayyana ra'ayin ta na kin son shugaba Muhammadu Buhari.
A baya dai mun samu cewa jarumar wadda yanzu haka tauraruwar ta ta dishe a masana'antar ta fito ta bayyana cewa dukkan mai dagewa akan son shugaba Buhari bai san mai ke masa ciwo ba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng