Harkar Girma: Mai kudin Duniya zai halarci daurin auren 'yar Dangote da dan tsohon shugaban 'yan sanda
- Hamshakin Dan kasuwa, Aliko Dangote, zai aurar da 'yar sa, Fatima, a watan Maris ga Jamil, dan tsohon shugaban hukumar 'yan sanda, MD Abubakar
- Ana saka ran mutumin da yafi kowa kudi duniya, Bill Gates, zai halarci daurin auren
- Kamar yadda sanarwa ta gabata, za'a daura auren ne a katafaren Otal din Eko dake garin Legas, a watan Maris, 2018
Wani gagarumin aure na nan tafe a watan Maris na shekarar nan, 2018, a garin Legas, a katafaren Otal, Eko Suite and Towers. Aure tsakanin Fatima dangote da Jamil abubakar.
Auren Fatima, diyar Aliko dangote, mafi kudi a nahiyar Afrika, da Jamil dan tsohon shugaban hukumar 'yan sanda ta kasa, MD abubakar, zai tattara masu hannu da shuni da kuma masu fada aji a daga ko ina a fadin Duniya.
Kamar Yadda rahotanni suka nuna, shugabanin kasashe biyar zasu halarta, har da hamsahakin maidukiya da babu kamarsa a duniya, wato Bill Gate.
DUBA WANNAN: An kuma: Tsohon shugaban kasa IBB ma ya aike da nasa sakon ga shugaba
An dade ana kishin-kishin din aure tsakanin Fatima da masoyinta Jamil, yanzu ta tabbata zasu saka lalle a cikin shekarar nan.
Rahotannin da jaridar Legit.ng ta samu basu ambaci ranar da za'a daura auren yaran manyan ba. Kazalika, ya zuwa yanzu, babu jadawalin yadda shagulgulan bikin zasu kasance ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng