An kuma: Tsohon shugaban kasa IBB ma ya aike da nasa sakon ga shugaba Buhari

An kuma: Tsohon shugaban kasa IBB ma ya aike da nasa sakon ga shugaba Buhari

- Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya aike da nasa rubutaccen sakon ga shugaba Buhari

- Babangida ya nuna rashin gamsuwar sa da kwazon shugaba Buhari a kan karagar mulki

- Ya fadawa shugaba Buhari kuru-kuru cewar ya cewar ba shine shugaban da Najeriya ke bukata ba

Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya aike da wani rubutaccen sakon ga shugaba Buhari inda yake shawartar sa da ya hakura da batun takarar shugabancin kasa a zaben shekarar 2019.

A wani jawabi da IBB din ya fitar a yau, Lahadi, ya bayyana rashin gamsuwar sa ga salon shugaba Buhari da ma jam'iyyar APC bakidaya.

Kazalika, ya goyi bayan yin garambawul ga tsarin mulkin Najeriya, musamman a bangaren rabon iko a tsakanin bangarorin gwamnati.

An kuma: Tsohon shugaban kasa IBB ma ya aike da nasa sakon ga shugaba Buhari
Tsohon shugaban kasa IBB

Babangida ya bayyana takaicinsa na gaza samun shugaba nagari a Najeriya da zai kawo canji na hakika a kan yadda al'amuran kasa ke gudana tare da shawartar Buhari cewar "lokaci ya yi da ya kamata ya ajiye bukatar kansa ya rungumi kishin kasa ta hanyar fasa tsayawa takara a zabe mai zuwa."

"Bisa ga yadda al'amura ke gudana, akwai bukatar mu goyawa shugaba Buhari baya ya kammala zangon mulkinsa da zai kare a watan Mayu, 2019 tare da hada kai da shi domin fitar da matashi daga cikin 'yan Najeriya da zai maye gurbinsa," A cewar Babangida, mutumin da ya mulki Najeriya daga shekarar 1985 zuwa shekarar 1993.

DUBA WANNAN: Obasanjo ya tuntube mu, kuma kaso 80% cikinmu na tare das hi – Sanatocin Arewa

Jawabin na IBB ya cigaba da cewar "Ina bayar da wannan shawara ne a matsayina na mai ruwa da tsaki a sha'anin mulkin Najeriya, a matsayina na tsohon shugaban kasa, da kuma dan kishin kasa dake son ganin kasar sa hau hanya madaidaiciya da zata tabbatar ta cigaba mai dorewa. Ina so jama'a su sani cewar, don na bayar da shawara, hakan ba yana nufin ina son yin kutse cikin 'yancin Buhari na tsayawa zabe ba kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya sahale masa, illa iyaka dai na san akwai lokaci da a rayuwa ya kamata mutum ya jingine bukatar kashin kansa domin inganta rayuwar kasar sa."

Wannan sako na Babangida na zuwa ne sati guda kacal bayan wasikar da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya aikewa Buhari yana shawartar sa da a'kul ya sake ya fito takarar shugabancin Najeriya a zaben 2019, kamar yadda jaridar Legit.ng ta rawaito maku.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng