Lauyoyi sun yi fashin baki kan hukuncin kotu kan korar Magu daga EFCC
- Majalisar Dattijai na son lallai sai Buhari ya kori Magu
- Magu ya gurfanar da Bukola Saraki ga kotun CCT
- An kai Magu kotu kan batun shugabantar EFCC

Wani lauya da ya shigar da kara kotun, kan ta fayyace masa, ko majalisa na da damar ta ki amincewa da zababben mutum daga gwamnati, kan kujerar EFCC ya sami hukuncin da yake bida.
Hukuncin dai ya ce, lallai majalisa na da damar kin amincewa da mutum muddin halinsa bayyi mata ba, laifin kuwa da majalisar ta zargi Magu da shi, shine cin hanci da rashawa.
Sai dai ana ganin kamar batun kai shugaban majalisar kotun CCT ne ya sanya majalisar tayi masa bita da kulli.
DUBA WANNAN: Yadda Obasanjo yake yi wa Buhari taron dangi kan 2019
Femi Falana dai, ya bi bayan lauyan da ire-irensa, inda ya ce ko da kotu ta goya wa majalisar baya, ai akwai kuma hukunci makamancinsa da ta yanke, wanda kuma ya bata laifi.
Kotun dai tace ko wadanda suka kai karar bassu da ma wata matsaya da zasu kai karar. Sannan kuma kotun ta ce sai an cire siyasa sannan za'a san inda aka kwana da batun.
A yanzu dai, shekaru kusan uku kenan da dora Magu a kujerar EFCC, sai dai majalisar ta ki amicewa ya zama na din-dindin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng